INFO:
Almajiri ne Dan Almajirai 💝💯 ـــــــــ Gwani Isa Kenan Sanye Da Kayan NYSC, Yake Rera Tilawar Al-Qur'ani Mai Girma Awajan Wata Musaffa Da Akayi A Garin GETSO GWARZO L.G.A Dake Jihar Kano Nigeria. ــــــــ Takaitaccen Tarihin Gwani Isa... ــــــ Cikekken sunan mallan shine Gwani Isa Muhammad Yusuf, shi dan asalin yobe State ne, Tarmuwa L.G.A Chirokusko Town Batoyi Ward, Yanazama a garin Kano unguwar Danladi Nasidi Quarters Karatun Qur-ani yafara a Maiduguri a gaban Mahaifa sai Mahaifinsa yakaishi Makarantar Malam Goni Sani Me Dubu a garin Maiduguri, Bayannan Shekara 1 shi Goni Sani me Dubu yakaishi kauyen Guro Soye dake Bama L.g.a Maiduguri. Bayan Kammala Rubutun Qur-ani nafarko sai Goni Sani Me Dubu yasake turashi Kano gurin amininshi Malam Goni Saminu Bachirawa. Ananne yayi Rubutun Qur ani na biyu tare da yin Ilimin Littafin Fiqhu a wurin Shek Mu-azu Bachirawa. Sai kuma mallan gwani Isa yadawo Boko karatun zamani, yayi Primary a Tarmuwa L.G.A Yobe State, yayi Secondary a Kano Queen Amina College, yayi Daura A Sudan, Mallan yayi Jamiar Maiduguri afannin Law Faculty of Law. Sai kuwa yayi Nigerian Law School a Bagauda Kano. mallam yayi ziyara zuwa kasashe dadama irinsu sudan, Saudi, Dubai, camaru, Chidi, Niger Da Dai Sauransu... Mallan gwani ISA yanzu yana zama a kano da Iyalin sa gidan sa yana wata unguwa nasidi kwatas, kuma yayi auren farko wata hudu dasuka wuce Wannan shine takai tatchen tarihin mallan gwani Isa mutunin kirki ne saima allah yasa wata mu,amala ta hadaku zaka kara tabbatarwa da haka. Allah Ya Karawa Rayuwa Albarka Yan Uwa Mu Kara Dagewa Da Karatu Na Addini Da Na Zamani Allah Ya Mana Jagora Daya.👏🏼